Yaran Kasar Siriya Sun gudanar Da zanga-zanga a yammacin Damuscus
Kananen Yara na Siriya sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewar su da killace garin Dariya dake gefen birnin Damuscus
Tashar Telbijin din Sky News ta habarta cewa a safiyar yauAlkhamis Kananen Yaran Siriyan sun gudanar da zanga-zanga domin nuna bacin ransu kan yadda ake ci gaba da killace garin Dariya dake gefen birnin Damuscus, wanda hakan ya yi sanadiyar hana isar taimakon abinci da kuma maguguna zuwa cikin garin.
Yayi da suke ishara kan mawuyacin halin da Al'ummar garin Dariya da ma wasu gariruwa dake kalkashin ikon 'yan ta'adda suka shiga, Yaran sun bukaci da a bar gayayyakin Agaji da suka hada da abinci, ruwan sha gami da magani suka shiga cikin wadanan gariruwa.
A wani rahoto da ta fitar jiya Laraba, kungiyar farar hula ta ceton kananen yara a siriyan, akalla kananen yara dubu 250 ke cikin mawuyacin hali sakamakon killace gariruwan da suke ciki a kasar Siriyan.
Rahoton ya ce kananen yara da dama suka hallaka sakamon matsalar karamcin abinci da kuma na rashin magani a gariruwan dake kalkashin killacewar kungiyoyin 'yan ta'adda a Siriyan.