Hamas Ta yi Maraba Da Harin Daukar Fansa Akan 'Yan Sahayoniya.
Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana harin da aka kai wa 'yan sahayoniya a matsayin maida martani kan wuce gonar da su ke yi.
Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana harin da aka kai wa 'yan sahayoniya a matsayin maida martani kan wuce gonar da su ke yi.
A jiya juma'a da dare ne dai wani matashi bapalasdine Umar Abdul Jalil al-abd, ya kai hari akan 'yan sahayoniya 3 inda ya halaka su nan take a gabacin Ramallah.
Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Palasdinu 'Hamas" ta fitar da bayani da a ciki ta bayyana cewa; Haramtacciyar Kasar Isra'ila ce ta ke da alhakin abinda ya faru saboda siyasarta ta wuce gona da iri da kuma nuna wa palasdinawa wariya."
A ranar 14 ga watan nan na yuli 'yan sahayoniyar sun hana yin sallar juma'a a cikin masallacin Kudus a karon farko cikin rabin karni.
A jiya juma'a ma dai 'yan sahayoniyar sun maida birnin Kudus sansanin soja inda su ka girke jami'an tsaro 2000 tare da kai wa palasdinawa hari a sassa daban-daban na birnin.