Wasu 'Yan Ta'addar Jabhatu-Nusra Sun Meka Kansu A Gabashin Labnon
Rahotanni dake fitowa daga kasar Labnon sun habarta cewa 'yan ta'adda na Jabhatu-Nusra sun meka kansu a wasu yankuna na Arisal dake gabashin kasar
Tashar Telbijin din Almayadin dake watsa shirye-shiryenta daga kasar Labnon ta habarta cewa yayin da aka shiga kwanaki na biyu da fara kai farmaki kan kungiyar 'yan ta'addar Jabhatu-Nusra, a marecen wannan Assabar, wasu mayakan 'yan ta'addar sun daga farin gyelle a yakin Ikabu-Dab, Wadil-Khail, na jihar Arisal da hakan ke nuna cewa mun meka wuya.
Rahoton ya kara da cewa wasu daga cikin mayakan na kungiyar Jabhatu-Nusra sun gudu sun bar makamansu a tsaunin Karnatul-Kanzah dake yankin na Arisal, a bangaren guda mayakan na Hizbullah sun samu nasarar shiga yankin Dahratul-Hawah, inda suka kafa tutar gwagwarmaya a yankin, bayan da suka saukar tutar kunngiyar ta'addancin nan ta Jabhatu-Nusra.
A jiya Juma'a ne dai dakarun kungiyar Hizbullah din da sojojin Siriya suka kaddamar da hare-haren kwato wadannan yankuna daga hannun 'yan ta'addan wadanda suke amfani da su wajen kai hare-hare cikin kasar Siriya da kuma Labanon din lamarin da dakarun na Hizbullah suka ce ba za su taba amincewa da hakan ba, musamman ganin cewa 'yan ta'addan sun mai da yankin na Arsal wata tungarsu da kai hare-haren ta'addanci kan yankunan da Hizbullah din suke da jama'a. Kungiyar dai ta ce ba za ta dakatar da wadannan hare-hare ba har sai sun tsarkake yankin daga dukkanin 'yan ta'addan.