'Yan Taliban Sun Kashe Sojojin Afganistan 26
Hukumomi a Afganistan sun ce sojojin kasar 26 ne suka rasa rayukansu a yayin wani hari da mayakan Taliban suka farma wa sansaninsu dake kudancin kasar.
Sanarwar da hukumomin suka fitar ta kuma ce an hallaka mayakan na Taliban 80, a yayin harin da suka kai kan sansanin a cikin tsakar daren jiya Talata, a cewar kakakin ma'aikatar tsaron kasar Janar Dawlat Waziri.
Bayanai daga hukumomin yankin sun ce an shafe sa'o'i masu yawa ana ta bata kashi tsakanin bangarorin biyu a sansanin sojin na Karzali dake yankin Kandahar a kudancin kasar ta Afganistan.
A baya bayan nan dai kungiyar taliban ta yunkuro da wani sabon salo na kai hare hare akan sansanonin soji da cibiyoyin 'yan sanda.
Kungiyar dai ta Taliban ta wallafa a shafinta na Twitter cewa iata keda alhakin kai harin, wanda a cewar ta ya yi sanadin mutuwar sojojin Afganistan din 70.