An sanar da ranar Zaben shugaban kasan Siriya
Manzon musaman na MDD kan Kasar Siriya ya ce nan da wattani 18 za a gudanar da zaben shugaban kasar Siriya.
Kamfanin dillancin Labaran kasar Iran ya nakalto Sataffan de Mistura manzon musaman na Babban saktaren MDD kan kasar Siriya na cewa samar da Gwamnatin hadin kai 'yan kasa shine babban abinda taron Ganeva zai fi maida hankali kansa kuma muna fatan cewa a tattaunawar farko za a cimma wannan matsaya ganin cewa bangarorin sun amince da gudanar da zaben shugaban kasa cikin wattani 18 masu zuwa.
De Mistura ya kara da cewa a kwai kudurori uku da kwamitin tsaro na MDD ya gabatar tare da amincewar magabatan kasar Rasha. yayin da yake ishara kan kuduri mai Lamba 2254, De Mistura ya bayyana cewa wannan kuduri ya hada da kafa sabuwar Gwamnati, sabunta Dokokin tsarin milkin kasar tare kuma da gudanar da zabe.
A ranar 14 ga watan Maris din da muke ciki ne za fara gudanar da taro kan kasar Siriyan a birnin Ganeva, inda ake sa ran za a kamala shi a ranar 20 ga watan.