Pakistan : An Zabi Shahid Khaqan Abbasi A Matsayin Sabon Firaminista
Majalisar dokoki a Pakistan ta zabi Shahid Khaqan Abbasi a matsayin sabon Firaminista bayan kotun kolin kasar ta tube Nawaz Sharif kan badakalar rashawa a makon jiya.
Majalisar ta dai zabi Abbasi na Jam’iyyar PML-N mai mulki da yawan kuri’u 221 a cikin 'yan majalisu 342 da zauren majalisar ya kunsa.
Da yammacin Yau Talata ne kuma ake sa ran Abbasi zai sha rantsuwar kama aiki.
Tun a cikin shekara 2013 ne Mista Abbasi ke rikeda mukamin ministan man fetur na kasar a karkashin gwamnatin Nawaz Sharif, kana kuma ya taba zama shugaban kamfanin jiragen saman kasar na kasa da kasa cewa da Pakistan International Airlines (PIA).
A ranar Juma’a ne, Nawaz Sherif ya yi murabus daga matsayin Firaministan kasar a karo na uku bayan kotun kolin kasar ta ce, za ta tube shi kan badakalar rashawa da ta shafe shi da iyalansa da ake zargin sun boye kudi a Panama ta hanyar amfani da wasu kamfanoni.