Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Espania
Babban Sakatarin kungiyar kasashen Larabawa ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai birnin Basalona na kasar Espania.
Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto Ahmad Abul-Ghaid yana fadar haka a yau jumma'a a wani bayani da ya fiyar, ya kuma kara da cewa dolene kasashen duniya su kara daura damara na yaki da ta'addanci.
Babban sakataren ya kara da cewa irin wannan harin kan mutanen da basu ji ba basu gani ba, ya sabawa dukkan abinda ake kira mutuntaka, ya kuma mika ta'aziyyarsa ga gwamnati da kuma iyalan wadanda harin ya shafa a kasar ta Espania. Ya kuma yi fatan saurin murmurewa ga wadanda suka ji rauni.
A jiya Alhamis ne wani dan ta'adda ya tuka motar bus ya hau kan wani titi cike da mutane a birnin Basalona na kasar Espania, ya kuma burma cikinsu ya kashe mutane 13 a take ya kuma raunata wasu 100. Kungiyar yan ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin kai harin na Basalona.