Qatar Ta Musunta Hana Jiragen Saman Saudiyya Sauka A Doha
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i23402-qatar_ta_musunta_hana_jiragen_saman_saudiyya_sauka_a_doha
Hukumar kula da kai-kawo na jiragen saman fasinja a Qatar ta musunta cewa ta hana jiragen saman Saudiyya sauka a Doha domin jigilar alhazai zuwa Makka.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 21, 2017 06:47 UTC
  • Qatar Ta Musunta Hana Jiragen Saman Saudiyya Sauka A Doha

Hukumar kula da kai-kawo na jiragen saman fasinja a Qatar ta musunta cewa ta hana jiragen saman Saudiyya sauka a Doha domin jigilar alhazai zuwa Makka.

Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu kafofin yada labarai na Saudiyyar suka ambato a jiya Lahadi cewa mahukuntan Qatar sun hana jigarensu sauka Doha domin jigilar alhazan.

Saidai hukumar dake kula da sinfirin jiragen sama ta Qatar ta ce wannan zargi ne wanda ba shi da tushe balla makama, kamar yadda kamfanin dilancin labaren kasar na QNA ya rawaito.

A tsakiyar makon jiya ne Sarki Salman na Saudiyya ya bada umurnin bude iyakokin kasarsa ga mahajjatan na Qatar domin yin aikin hajji, duk da rikicin diflomatsiyya na tsakanin kasashen biyu.