Masarautar Bahrain Na Ci Gaba Da Killace Yankin Al-Duraz
Jami'an tsaron masarautar Al Khalifa da ke rike da madafun iko a kasar Bahrain suna ci gaba da killace yankin Duraz musamman gidan baban malamin addini na kasar Sheikh Isa Qasim.
Shafin yada labarai na shafaqana ya bayar da rahotopn cewa, matasan yankin Duraz sun saka hotuna a shafuka na yanar gizo da ke nuna halin da yankin yake ciki a halin yanzu, tun bayan farnakin da jami'an tsaron masarautar kasar suka kai da nufin tarwatsa masu zaman dirshan a kofar gidan babban malmin addini na kasar Sheikh Isa Kasim.
Bayan kashe fararen hula 'yan kasa da kuma jikata wasu da dama da kume kame wasu, jami'an tsaron sun ci gaba da zama a wurin, inda suka killace gidan shehin malamin tare da hana shi fitowa, da kuma yanke duk wata alaka a tsakaninsa da al'ummar kasar.
Masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain dai tana zargin Sheikh Isa Kasim da mara baya ga 'yan kasar masu neman hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu na 'yan kasa, ta fuskar siyasa da kuma zamantakewa da amfana arzikin kasarsu.