Unicef: Fiye Da Yaran Kasar Yemen 1700 Ne Suka Rasa Rayukansu
Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Yemen ya ce; Daga lokacin da Saudiyya ta fara hari zuwa yanzu, an kashe yara fiye da 1700.
Meritxell Relano wanda tashar telbijin din Russia Today, ta yi hira da shi a jiya talata ya ambaci adadin yaran da yakin na Saudiyya ya kashe a Yamen, sannan ya kara da cewa wasu yaran da suka kai 3000 sun jikkata.
A cikin watanni biyu na bayan nan kadai, yara 38 ne suka rasa rayukansu a kasar ta Yemen.
Relano ya kuma ce; hanya daya ta dakatar da kashe kananan yara ita ce ta kawo karshen yakin.
Har ila yau, jami'in na asusun kananan yaran ya ambaci wahalar da ake sha wajen isar da kayan agaji cikin kasar ta Yemen.
Tun a 2015 ne dai Saudiyyar ta shelanta yaki a kasar Yamen tare da killace dukkanin hanyoyin kasar na sama da ruwa da kuma kasa.