Aug 31, 2017 12:44 UTC
  • Isra’ila Na Shirin Gina Sabbin Matsugunnan Yahudawa A Birnin Quds

Haramtacciyar kasar Isra’ila na da shirin gina wata sabwar unguwa ta yahudawa a cikin yankunan palastinawa da ta mamaye a cikin birnin quds.

Shafin yada labarai ta tashar Palastine Yaum ya bayar da rahoton cewa, ministan tsaron cikin gida na Isra’ila Gilad Ardan tare da wasu jami’ai sun yi wani rangadi a cikin birnin Quds domin duba yadda za a fara aiwatar da wannan shirin.

Tashar talabijin ta bakwai ta Isra’ila ta bayar da rahoton cewa, babbar manufar wananns hiri ita ce gina wasu sabbin matsugunnai na musamman a wasu yankuna da ke cikin birnin Auds, wadada za a kebance su ga jami’an tsaro kawai.

Wannan dai yana da cikin shirin da Isra’ila take da shin a tabbatar da cewa ta mamaye birnin Quds baki daya, tare da mayar da Palastinawa saniyar ware a cikin birnin mai tsohon tarihi.

Tuni Isra’ila ta fara daukar matakai na ganin ta kara fadada matsugunnan yahudawa har a cikin yankunan gabashin Quds wanda mazauna yankunan Palastinawa ne zalla. Kamar yadda a halin yanzu an kafa shingayen tsaro a dukkanin yankuna da tituna na birnin har da manyan titunan da ke gefen masallacin aqsa mai alfarma.

Tags