Kasashen Sudan Da Qatar Sun Jaddada Muhimmancin Karfafa Alaka A Tsakaninsu
(last modified Sat, 16 Sep 2017 11:51:09 GMT )
Sep 16, 2017 11:51 UTC
  • Kasashen Sudan Da Qatar Sun Jaddada Muhimmancin Karfafa Alaka A Tsakaninsu

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ya bada labarin cewa: Mahukuntan Sudan da Qatar sun tattauna kan hanyoyin bunkasa alaka tare da taimakekkeniya a tsakaninsu.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sudan Qaribullahi Khidir ya bayyana cewa: Jami'an kasashen Sudan da Qatar sun tattauna kan hanyoyin gudanar da taimakekkeniya da bunkasa alaka a tsakaninsu da nufin ci gaban kasashensu.

Har ila yau Qaribullahi Khidir ya kara da cewa: Jami'an kasashen biyu zasu sake gudanar da wani zaman tattaunawa a tsakaninsu a birnin Doha na kasar Qatar a watan Oktoba mai zuwa da nufin karfafa alakar kasashensu.

Qaribullahi ya fayyace cewa: Sudan ba zata shiga cikin dambaruwar siyasar da ke tsakanin wasu kasashen Larabawa da Qatar ba, don haka tana goyon bayan shiga tsakani da kasar Kuwait ke yi a tsakanin kasashen da Qatar.