Basshar Asad: Har Yanzu Wasu Kasashen Turai Na Taimakawa 'Yan Ta'adda
Sep 17, 2017 08:00 UTC
Shugaban na Kasar Syria ya fadi hana ke a yayin da yake ganawa da tawagar Majalisar Dokokin Italiya a birnin Damasacuss.
Shugaban na kasar Syria ya ci gaba da cewa; Tare da cewa al'ummun wasu kasashen turai suna fama da matsalar ta'addanci, amma gwamnatocinsu suna ci gaba da taimakawa 'yan ta'adda.
Shugaba Assad, ya kuma ce ziyarar da jami'an na kasashen turai suke kai wa Syria za ta iya taimakwa domin sauya tunanin al'ummar kasarsu da gwamnatoci dangane da hakikanin abubuwan da suke faruwa a cikin kasar ta Syria.
Tawagar 'yan majalisar kasar Italiya da take ziyara a kasar Syria tana karkashin jagoranci shugaban majalisar dattijai ne Mario Romani.
Tags