An Kashe Kwamandojin Da'esh A Arewacin Kasar Iraki
Sep 28, 2017 06:48 UTC
Tashar telbijin din al'alam ta bada labarin cewa kwamandojin kungiyar ta 'yan ta'adda 7 ne suka halaka a harin da sojojin suka kai a garin Hawijah a jiya laraba.
Cibiyar da ke bada labarun yaki ta Iraki ta ce, wadanda aka kashe din sun hada da masu bada kariya ga Abubakar Bagadadi, shugaban kungiyar ta 'yan ta'adda.
Daga lokacin da sojojin Iraki suka fara kokarin kwato garin Hawijah zuwa yanzu sun kashe fiye da 'yan ta'adda 500.
Bayan 'yanto da garin Talla'afar da sojojin Iraki suka yi daga hannun 'yan ta'addar Da'esh, sojojin kasar suna kan kokarin kwato garin Hawija da ke kudancin garin Karkuk.
Tags