Sarki Salman Na Saudiyya Zai Ziyarci Rasha
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i24565-sarki_salman_na_saudiyya_zai_ziyarci_rasha
Wani mashawarci a fadar shugaban kasar Rasha ya tabbatar da ziyarar da sarki Salman na Saudiyya zai kai a kasar a ranar Alhamis mai zuwa.
(last modified 2019-08-10T14:54:46+00:00 )
Oct 02, 2017 17:34 UTC
  • Sarki Salman Na Saudiyya Zai Ziyarci Rasha

Wani mashawarci a fadar shugaban kasar Rasha ya tabbatar da ziyarar da sarki Salman na Saudiyya zai kai a kasar a ranar Alhamis mai zuwa.

Kamfanin dilancin labaren Rasha na TASS ya rawaito Iouri Ouchakov na fadar hakan sai dai ba tare da yin karin haske ba.

kafin hakan dai ma'aikatar yada labarai ta Sudiyya ta danganta ziyarar ta sarkin mai shekaru 81 da mai matukar mahimmanci, wacce kuma ita zata kasance ziyara ta farko da wani sarkin Saudiyya zai kai a Rasha.

A nasa bangare kuwa kamfanin dilancin labaren Saudiyya na SPA ya nakalto cewa ziyara ta sarki Salman bisa goron gayyatar shugaban Rasha Valdimir Putin za ta maida hankali kan yadda za'a karfafa hulda tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi yankin dana kasa da kasa.

Kasashen Rasha da Saudiyya dai na da sabani akan batutuwan da shuka shafi Yemen da kuma Siriya.