Sarkin Saudiyya Na Ziyara A Rasha
Oct 05, 2017 09:48 UTC
Sarki Salman bin Abdul-Aziz na Saudiyya ya sauka a birnin Moscow a wata ziyara da ita ce irinta ta farko da wani sarki na Saudiyya ya kai kasar Rasha.
Kamfanin dilancin labaren Saudiyya na SPA ya rawaito cewa, Sarkin na ziyara ne bisa goron gayyatar shugaban kasar Rashar Vladimir Putin.
Bangarorin biyu zasu maida hankali kan karfafa hulda tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan da suka shafi yankin dama na kasa da kasa.
Kasashen Rasha da Saudiyya dai na da sabani akan batutuwan da shuka shafi Yemen da kuma Siriya.
Tags