Iraki: "Rasul Ali" Zai Zama Magajin Jalal Talibani A Jam'iyyar "PUK"
Oct 08, 2017 04:51 UTC
Wani jami'i a jam'iyyar "Patriotic Union of Kurdistan" Giyath al-Surjy, ya ce; Kosrat Rasul Ali ne zai maye gurbin Jalal Talibani a shugabancin jam'iyyar.
Giyath al-Surjy ya ci gaba da cewa; A karkashin dokokin jam'iyyar idan babban sakatarenta ya rasu ko ya yi murabus, to mataimakinsa na farko zai gaje shi. A halin yanzu Rasul Ali ne mataimaki farko don haka zai zama babban sakataren jam'iyyar har zuwa lokacin da za a yi zabe.
Jalal Talibani wanda shi ne shugaban kasar Iraki na farko da ba balarabe ba. Ya rasu a makon da ya gabata, inda aka yi jana'izarsa a mahaifarsa ta Sulaimaniyya.
Ya rasu yana dan shekaru 84.
Tags