MDD Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Sulhu Tsakanin Fatah Da Hamas
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i24873-mdd_ta_yi_maraba_da_yarjejeniyar_sulhu_tsakanin_fatah_da_hamas
Majalisar Dinikin duniya ta yi maraba da yarjejeniyar sulhun da kungiyoyin Fatah da Hamas suka daddale tsakaninsu a kasar Masar.
(last modified 2018-08-22T11:30:49+00:00 )
Oct 13, 2017 04:48 UTC
  • MDD Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Sulhu Tsakanin Fatah Da Hamas

Majalisar Dinikin duniya ta yi maraba da yarjejeniyar sulhun da kungiyoyin Fatah da Hamas suka daddale tsakaninsu a kasar Masar.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya tattauna da shugaban Palestinawa Mahmoud Abbas ta wayar tarho, inda ya taya shi murnar daddale wannan yarjejeniyar.

Wata sanarwa da ofishin kakakin babban sakataren ya fitar, ta ce Antonio Gutarres ya yi farin ciki matuka bisa ci gaban da gwamnatin Palestinu ta samu a zirin Gaza, ya na mai jinjinawa gwamnatin kasar Masar bisa kokarin shiga tsakanin da ta yi kan batun.

Antonio Guterres ya ce, a shirye MDD take ta taimakawa gwamnatin Palestinu yayin da take gudanar da harkokin zirin Gaza, wanda zai taimaka wajen muhimmancin warware wasu mahimman batutuwa a zirin, da suka hada da samar da wutar lantarki, da jigilar kayayyakin jin kai.

A jiya ne dai Kungiyoyin Fatah da Hamas suka cimma yarjejeniyar sulhu tsakaninsu a birnin Alkahira na kasar Masar bayan shafe tsawon yini biyu na tattaunawa.

Bangarorin biyu dake gaba da juna a cen baya sun amunce cewa daga ranar 1 ga watan Disamba mai zuwa kungiyar Fatah ce za ta fara gudanar da harkokin zirin Gaza a maimakon Hamas.