Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Kurdawa
Oct 21, 2017 18:21 UTC
Tashar telbijin din al'alam ta nakalto cewa; Pira ministan haramtacciyar Kasar Isra'ila yana ci gaba da nuna goyon bayansa ga kokarin ballewar Kurdawa.
Cibiyar labaru ta Meadle-east Online ta ce wani jami'in haramtacciyar kasar Isra'ila da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce; Isra'ila tana da moriyar da za ta ci ta fuskar tsaro a kafuwar kasar Kurdawa, saboda kusancinta da Iran da kuma Syria.
Majiyar ta ci gaba da cewa; Tun a lokaci mai tsawo haramtacciyar kasar Isra'ila take da alaka ta kasuwanci da cinikayya da Kurdawa.
Kawo ya zuwa yanzu babu wanda ya goy bayan ballewar kurdawan Iraki domin kafa kasa, sai haramtacciyar kasar ISra'ila.
Tags