Hamas: Ba Za Mu Taba Watsi Da Makamai Ba.
Shugaban Kungiyar Hamas a yankin Gaza Yahya Sinwar ya ce; Makamin da yake hannun kungiyar ta Hamas mallakin dukkanin palasdinawa ne.
Yahya Sinwar wanda ya gana da wakilan kungiyoyin palasdinawa daban-daban a jiya talata a yankin Gaza,ya ci gaba da cewa; makaman da suke a hannun Hamas, mallakin daidaikun kananan yara da mutanen palasdinu ne, don haka babu wani lokaci da za a ce al'ummar Palasdinu ba ta da bukatar makamai.
Da yake magana akan sulhun da aka yi a tsakanin Hamas da kungiyar Fatah, Sinwar ya ce; Idan har kungiyar ta Fatah tana da kaso 20% na kyakkyawar niyyar kungiyar Hamas, to duk wani sabani zai bace.
Har ilayau jagoran na kungiyar Hamas ya ce; idan har makiya suka yi kokarin kawo cikas a sulhun na Palasdinawa, to za su yi nadama.
A ranar 12 ga watan Oktoba ne aka yi yarjejeniyar sulhu a tsakanin Hamas da Fatah a birnin alkahira.