Mas'ud Barzani Ya Ce Zai Sauka Daga Shugabancin Yankin Kurdawa
(last modified Sun, 29 Oct 2017 19:01:59 GMT )
Oct 29, 2017 19:01 UTC
  • Mas'ud Barzani Ya Ce Zai Sauka Daga Shugabancin Yankin Kurdawa

A wani jawabi da ya gudanar dazun nan ta hanyar kafafen watsa labaru,Barzani ya tabbtar da cewa zai sauka daga farkon watan Nuwamba mai zuwa.

Tun da fari Mas'ud Barzani ya aike da wasika zuwa ga  majalisar dokokin yankin na kurdawan wacce aka karanta zaman da ta yi a yau lahadi da a ciki ya bukaci majalisar yankin ta dauki matakan doka da suka dace domin hana afkuwar gibi na mulki.

Barzani ya bayyana kansa a matsayin daya daga cikin mayakan kurdawa na Peshmarga da zai ci gaba da gwagwarmaya a tare da sauran mutane har zuwa samarwa da Kurdawa cikakken hakkokinsu.

Mas'ud Barzani zai yi murabus ne ranar farko ta watan Nuwamba mai zuwa.

Kuri'ar raba gardamar da aka kada a yankin Kurdawa ta jawo cecekuce, sannan kuma ta sa Kurdawan sun yi asarar yankuna da dama da suke rike da su a baya.