Sojojin Siriya Sun Kwace Daukacin Ikon Birnin Deir Ezzor
Rundunar sojin gwamnatin Siriya ta yi nasarar kwace daukacin ikon birnin Deir ez-Zor wanda shi ne babban birnin lardin dake gabashin kasar .
Wannan dai wata nasara ce babu tamakarta a yakin da sojojin kasar ke yi da 'yan ta'adda na kungiyar Da'esh.
Haka kuma, sojojin gwamnatin kasar sun hallaka mayakan kungiyar IS da dama, baya ga makamai da kuma harsashinsu masu yawa da suka kwace daga hannun mayakan.
A halin yanzu sojojin suna bincike don gano nakiyoyin da 'yan ta'addan na kungiyar ta IS ko Da'esh suka binne a titunan birnin, kamar yadda wata gidan talabijin din kasar ya sanar.
Wannan dai babban kalubale ga kungiyar ta Da'esh ta data jima tana aikata ayyukan ta'adi a wannan kasa ta Siriya dama wasu sassan yankin.
Wannan daina zuwa ne bayan da su ma sojojin kasar Iraki suka sanar da korar 'yan ta'addan na Da'esh a garin Ka'ima da ke yammacin gundumar Anbar.