Sojojin Siriya Sun Kwace Bukamal, Birnin Karshe A Hannun IS
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25384-sojojin_siriya_sun_kwace_bukamal_birnin_karshe_a_hannun_is
Rundinar sojin Siriya ta yi nasara kwace Bukamal, birnin na karshe da ke hannun 'yan ta'adda na IS gabashin kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Nov 09, 2017 00:59 UTC
  • Sojojin Siriya Sun Kwace Bukamal, Birnin Karshe A Hannun IS

Rundinar sojin Siriya ta yi nasara kwace Bukamal, birnin na karshe da ke hannun 'yan ta'adda na IS gabashin kasar.

Birnin Boukamal shi ne wani sansani na karshe inda sauren 'yan ta'addan na IS suka buya bayan fatatakarsu daga yankin Deir Ezzor na Siriya da kuma birnin Al-Qaïm na Iraki.

Baynai sun nuna cewa an murkushe 'yan ta'addan a cikin gajeren lokaci, ba kamar yadda akayi tsammani ba tun da farko cewa yakin zai yi tsanani, duk da cewa dai dakarun Rasha hadin gwiwa da na Siriya sun yi amfani da mayan dabaraun yaki.

Ko baya ga hakan bangarorin sun samu dauki daga mayakan kungiyar Hezbollah na Labanon, sannan daga wani bangaren sun samu dauki daga mayakan sa kai na 'yan shi'a a iyaka da Iraki.

Kwace birnin Boukamal, ya sanya a yanzu kungiyar IS ba ta rike da gari ko guda a Iraki da Siriya.