Yemen : Har Yanzu Akwai Cikas Wajen Shigar Da Kayan Agaji_MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa har yanzu kawancen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen na ci gaba da hadasa cikas wajen shigar da kayen agaji a wannan kasa.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kawancen ya sake bude tashar ruwan Aden dake kudancin kasar da kuma wata hanyar kasa ta Wadea mai matukar muhimmanci.
Kakakin hukumar kula da ayyukan jin kai na MDD (Ocha), Russell Geekie ya ce har yanzu akwai cikas wajen shigar da kayan agaji, don kuwa bude tashar ruwa ta Aden bai isa ba, suna bukatar a bude duk iyakokin kasar ta Yemen ciki har da Hobeida don shigar da kayan agaji da kuma harkokin kasuwanci.
Rufe iyakokin da Saudiyya ta yi a farkon makon nan, ya sanya MDD ta nuna damuwarta kan ukubar yunwa da kan iya kara afka wa kasar ta Yemen.
MDD ta bayyana halin da ake ciki a kasar Yemen da iftila'i mafi muni a duniya, inda mutane miliyan 17 ke bukatar agajin gaggawa na abinci, wandanda miliyan bakwai daga cikinsu ke fuskantar barazana yunwa.