Labanon : Aoun, Ya Bukaci Bayani Daga Saudiyya Kan Batun Hariri
(last modified Sat, 11 Nov 2017 15:23:20 GMT )
Nov 11, 2017 15:23 UTC
  • Labanon : Aoun, Ya Bukaci Bayani Daga Saudiyya Kan Batun Hariri

Shugaban kasar Labanon, Michel Aoun, ya bukaci bayani daga gwamnatin Saudiyya akan abunda ke kawo cikas wajen komawar firayi ministan kasar mai murabus Saad Hariri komawa gida.

Murabus din ba- zata da Hariri ya yi tun daga kasar Saudiyya a ranar hudu ga watan nan na Nuwamba ya sake jefa kasar ta Labonan cikin wani sabon rudanin siyasa.

Kuma tun lokacin ne ake nuna shakku akan ko Hariri yana cikin yancin tafiyar da rayuwarsa a kasar ta Saudiyya, bayan da wasu bayanai suka ce Saudiyyar ce ta cilasta masa yin murabus.

Har yanzu dai shugaban kasar ta labanon ya ki ya amunce da murabus din Hariri, yana mai cewa sai ya tattauna da shi tukuna.

A wani jawabinsa a jiya Juma'a shugaban kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrollah ya zargi Saudiyya da tsare Hariri kuma su suka cilasta masa yin murabus.