Labanon : Ina Cikin 'Yancin Walwala A Saudiyya_Hariri
A karon farko, tun bayan murabus dinsa na ba zata tun daga Saudiyya, firayi ministan Labanon, Saad Hariri, ya yi jawabi a gidan talabajin.
A jawabinsa a gidan talabijin na (FUTURE TV) mallakinsa, Mista Hariri ya ce zai koma kasarsa Labanon nan bada dadewa ba, tare da musunta bayyanan cewa bai da 'yancin walwala a Saudiyya, sannan ya ce murabus dinsa na da nasaba ne da hadarin da kasar ta Labanon take fuskanta.
An dai nuna hoton Hariri ya na jawabi a gajiye, sannan yana dari-dari a cikin karanto jawabin nasa na daren jiya Lahadi.
Hariri wanda yake ta tikar ruwa a lokacin jawabinsa, ya ce lalle murabus dinsa tun daga ketare ya sabawa tsarin mulkin amman zai mikawa shugaban kasar murabus dinsa idan ya koma Beyrut cikin kwanaki masu zuwa.
Wadannan kalaman na Hariri na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban kasar ta Labanon, Michel Ayun, ya bukaci bayyani daga Saudiyya kan halin da firayi ministan mai murabus ya ke ciki, tare da cewa da wuya ma in yana da yancin walwala a kasar.
Jawabin na Hariri dai ya jefa 'yan kasar Labanon da dama cikin shakku, kasancewar ba Haririn da suka sanni ba ne a da, don har kwalla ya zubda a lokacin jawabinsa.