Ministan Shari'a Na Pakistan Ya Yi Murabus
(last modified Mon, 27 Nov 2017 06:33:17 GMT )
Nov 27, 2017 06:33 UTC
  • Ministan Shari'a Na Pakistan Ya Yi Murabus

Minsitan shari'a na kasar Pakistan, Zahid Hamid, ya mika takardar murabus dinsa ga firayi ministan kasar Shahid Khaqan Abbasi.

Mika murabus din na Mista Hamid na zuwa ne makwanni uku na zanga-zangar da masu fafatukar islama na kasar ke yi.

Kamfanin dilancin labaren APP na Pakistan ya ce ministan ya mika murabus din ne bisa rajhin kansa domin kawo karshen rikicin da kasar ke fama da shi.

Tun a ranar 6 ga watan nan ne wasu 'yan kasar galibi na kungiyar Tehreek-i-Labaik Yah Rasool Allah (TLYRAP),a takaice ke mamaye da titin dake zuwa Islamabad babban birnin kasar kan wata ayar doka data shafi rantsuwa da ya kamata dan takara zabe ya yi, inda zai gama da shaida cewa Annabi Muhammad (SAW) bawan Allah ne kuma ma'aikinsa.

A kasar ta Pakistan dai akwai 'yan darikar ''Ahmadiyya'' wadanda su basu amince cewa Manzon Muhammad (SAW) shi ne ma'aikin Allah na kasrhe, don haka suke bukatar a kawo sauyi a cikin rantsuwar.