Hamas: Ba Za Mu Yarda Da Ajiye Makamai Ba
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i25795-hamas_ba_za_mu_yarda_da_ajiye_makamai_ba
Jami'in Kungiyar gwgawarmaya ta Hamas, Mahmud Zahar ya bayyana cewa; Babu wani mutum daya a cikin 'yan kungiyar ta Hamas da ya aminta da batun kwance damarar yaki.
(last modified 2018-08-22T11:31:03+00:00 )
Nov 27, 2017 11:55 UTC
  • Hamas: Ba Za Mu Yarda Da Ajiye Makamai Ba

Jami'in Kungiyar gwgawarmaya ta Hamas, Mahmud Zahar ya bayyana cewa; Babu wani mutum daya a cikin 'yan kungiyar ta Hamas da ya aminta da batun kwance damarar yaki.

 Zahar ya bayayna haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarun "Nabaa Press" sannan ya kara da cewa; Ba mu gaskata kungiyar Fatah ba cewa za ta aiwatar da yarjejeniyar da aka yi a bayannan,, amma duk da haka za mu ci gaba a da aiki da ita.

Zahar ya ci gaba da cewa; Matukar gwamnatin kwarya-kwarya ta Palasdinu ba ta biya albashin ma'aikata na watan Decemba ba, to Hamas za tana da matakan da za ta dauka.