Labanon : Hariri Ya Jingine Murabus Dinsa
(last modified Tue, 05 Dec 2017 17:21:12 GMT )
Dec 05, 2017 17:21 UTC
  • Labanon : Hariri Ya Jingine Murabus Dinsa

Firayi ministan kasar Labanoon, Saad Hariri, ya jingine takardar murabus dinsa, wata guda bayan sanar murabus din tun daga ksar Saudiyya.

Mista Hariri ya sanar da hakan ne a yayin da yake karanto wata sanarwar gwamnatin kasar a yau Talata, a yayin taron majalisar ministocinsa na farko da ya halarta tun bayan komawarsa kasar. 

Wannan matakin dai na Hariri zai kawo dan sauyi a rikicin siyasa dana tattalin arziki da murabus din nasa ya janyo a wannan kasa ta Labanon.

Majalisar ministocin kasar dai ta yabawa Hariri akan soke murabus din na sa.

Taron majalisar ministocin ya fitar da sanarwar cewa bangarorin siyasa na kasar za su nisanci tsoma baki a rigingimu da yake yake a yankin, da kuma harkokin cikin gida na kasashen Larabawa, a wani mataki na karfafa alaka siyasa da tattalin arziki tsakaninta da 'yan uwanta larabawa.