Sabon Zagayen Tattaunawa Kan Rikicin Siriya A Astana
Dec 21, 2017 06:15 UTC
Yau Alhamis ake sake komawa wani sabon zagayen tattaunawa a birnin Astana na Kazakhstan kan rikicin kasar Siriya tsakanin wakilan 'yan adawa da na gwamnatin kasar.
Mayan batutuwan da zaman zai maida hankali a kai sun hada da batun mutanen da ake tsare da su da fursunoni da isar da kayan agaji da kuma halin da ake ciki a yankunan da aka ayyana a mastayin ''tuddan mun tsira'' a kasar ta Siriya.
A gobe Juma'a ne ake sa ran fitar da sanarwar karshen zaman da kasashen Rasha da Turkiyya da Iran ke shiga tsakani.
Tags