Palasdinu: Wani Matashi Guda Ya Yi Shahada A Gabacin Yankin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i26669-palasdinu_wani_matashi_guda_ya_yi_shahada_a_gabacin_yankin_gaza
Ma'aikata kiwon lafiya ta Palasdinu ta sanar da shahadar Muhammad Sami Dahduh sanadiyyar harbin da 'yan sahayoniya suka yi masa
(last modified 2018-08-22T07:01:11+00:00 )
Dec 24, 2017 15:21 UTC
  • Palasdinu: Wani Matashi Guda Ya Yi Shahada A Gabacin Yankin Gaza

Ma'aikata kiwon lafiya ta Palasdinu ta sanar da shahadar Muhammad Sami Dahduh sanadiyyar harbin da 'yan sahayoniya suka yi masa

Cibiyar tattara bayanai ta Palasdinu ta kuma kara da cewa wani matashin bapalasdine wanda ya jikkata a harin da yan Sahayoniya suka kai masa a makon da ya wuce a gabacin Jabaliya, ya yi shahada a yau lahadi.

Yahudawa 'yan share wuri zauna da sojoji suke goyawa baya sun kai hari a kauyen Madama da ke kudancin Nablus tare da jikkata palasdinawa shida.

Makwanni biyu a jere kenan da palasdinawa suke gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da matakin shugaban kasar Amurka na bai wa 'yan Sahayoniya birnin kudus a matsayin birninsu.