Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Mutane Akalla 9 A Kasar Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i2677-harin_ta'addanci_ya_lashe_rayukan_mutane_akalla_9_a_kasar_iraki
Mahukuntan Iraki sun sanar da mutuwar mutane akalla 9 tare da jikkatan wasu fiye da 20 na daban sakamakon hare-haren ta'addancin da aka kai a wasu yankunan kasar a yau Asabar.
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 19, 2016 16:01 UTC
  • Harin Ta'addanci Ya Lashe Rayukan Mutane Akalla 9 A Kasar Iraki

Mahukuntan Iraki sun sanar da mutuwar mutane akalla 9 tare da jikkatan wasu fiye da 20 na daban sakamakon hare-haren ta'addancin da aka kai a wasu yankunan kasar a yau Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa; Wani bom ya tashi a kusa da wata kasuwa a kauyen Mahmudiyya da ke kudancin kasar Iraki, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 2 tare da jikkatan wasu 7 na daban.

Har ila yau wasu 'yan bindiga dadi sun kai harin wuce gona da iri kan wani gida a kauyen Mada'in da ke kudancin kasar, inda suka kashe mutane akalla 6 iyalan gida guda.

Haka nan wani tashin bom a yankin Hayyul-Amal da ke kudu maso yamma da birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki ya lashe ran mutum guda tare da jikkata wasu adadi masu yawa.