Mayakan Kungiyar Daesh Kimanin 300 Ne Suke Boye A Kasar Turkiya
Kasar Britania ta bayyana damuwarta da dawowan yan ta'adda mambobi a kungiyar Daesh wadanda a halin yanzu suke boye a kasar Turkiya.
Jaridar "Times " ta kasar Britania ta rubuta a shafinta a jiya laraba kan cewa daruruwan yan kasashen turai ne suke samun mafaka a kasar Turkiya bayan fatattakarsu daga kasashen Siriya da Iraqi, kimani 300 daga cikinsu yan kasar Britania ne.
Jaridar ta kara da cewa yan kasar Britania kimanin 850 suka shiga kungiyan yanta'adda ta Daesh kuma suka je kasashen Syria da Iraqi don yakar gwamnatocin kasashen, an kashe 130 daga cikinsu a yayin da wasu sun koma gida amma har yanzun wasu daga cikinsu na boye a kasar Turkiya.
A halin yanzu dai kasashen turai wadanda suka bar yan kasashensu suka shiga kungiyar Daesh, da kuma saninsu wadanda yan ta'adda suka fice daga kasashen zuwa kasashen Siriya da Iraqi don kifar da gwamnatin wadannan kasashen suna cikin zullumi, don basu san abin zai faru idan wadanda yan ta'adda sun dawo gida ba.
Kasashen yamma da dama sun taimakwa wadannan yan ta'adda wajen yakar halattattun gwamnatocin wadannan kasashen don cimma munanan manufofinsu a yankin gabas ta tsakiya .