Saudiyya: Ma'aikatar Shari'a Ta Tabbatar Da Kame Yarimomi 11
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27079-saudiyya_ma'aikatar_shari'a_ta_tabbatar_da_kame_yarimomi_11
Babban mai shigar da kara na kasar ta Saudiyya ya ce an kame yarimomin 11 ne bayan da suka yi gangami a bakin fadar mulkin kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:15+00:00 )
Jan 07, 2018 03:02 UTC
  • Saudiyya: Ma'aikatar Shari'a Ta Tabbatar Da Kame Yarimomi 11

Babban mai shigar da kara na kasar ta Saudiyya ya ce an kame yarimomin 11 ne bayan da suka yi gangami a bakin fadar mulkin kasar

Majiyar gwamnatin kasar ta ce yarimomin sun yi gangamin ne domin su nuna kin amiincewa da janye ba su ruwa da wuta kyauta da ake yi a kasar.

Saudiyya ta fito da shirin tsuke bakin aljihu da ya hada da dakatar da garabasar da yarimomin kasar suke ci na tsawon shekara da shekaru.

Koma bayan kudaden shiga da Saudiyyar ta fuskanta saboda faduwar farashin man fetur,da kuma yakin da take yi da kasar Yemen, sun tilasta masa daukar matakan tsuke bakin aljihu.