An Fice Da Yarimomin Saudiya Zuwa Gidan Yari Na Al-Ha'ir
Kimanin yarimomi da tsfin hukumomin saudiya 60 ne aka dauke da wurin da ake tsare da su zuwa gidan yari na Alha'ir.
Kafar watsa labaran Al'arabie Jaded wacce ake bugawa a birnin Landon ta nakalto wata majiya daga saudiya na cewa daga cikin mutanan da aka fice da su gidan yarin na Alha'ir akwai hamshakin mai kudin nan kuma yarima na saudiya Walid bn Talal, da Turki bn Abdul-Azez tsohon gwamnan birnin Riyad da kuma wasu manyan hukumomin kasar da suka ki amincewa da bukatar yarima mai jiran gado na mayar da wasu kudade a bitalamanin kasar.
Jaridar ta ce Walid bn Talal na daga cikin wadanda suka ki amincewa da kudirin yarima mai jiran gado tare da bukatar a gurfanar da shi tare da abokaninsa a gaban kuliya domin su kare kansu kan Zarkin da ake yi musu, lamarin da ya jefa yarima mai jiran gado cikin damuwa.
A baya dai, Ma'aikatar shari'ar kasar Saudiyya ta sanar da cewa da dama daga cikin 'ya'yan gidan sarautar kasar da sauran masu kudin da ake tsare da su bisa zargin rashawa da cin hanci sun amince da wata yarjejeniya ta kudi da aka cimma da su kafin daga bisani aka sake su daga wurin da ake tsare da su.