UNICEF: Saudiyya Ta Kashe Yara Dubu Biyar A Kasar Yemen
(last modified Sun, 14 Jan 2018 11:49:34 GMT )
Jan 14, 2018 11:49 UTC
  • UNICEF: Saudiyya Ta Kashe Yara Dubu Biyar A Kasar Yemen

Asusun kananan yara na MDD ta bakinsa shugabansa na arewacin Afirka ya ce;Kawo ya zuwa yanzu kananan yara 5000 Saudiyya ta kashe a cikin kasar Yemen

A yau lahadi ne Geert Cappeleere a ofishin UNICEF da yake a birnin Amman na kasar Jordan ya fitar da sanarwar wacce ta ci gaba da cewa; Kananan yaran ne wadanda aka fi cutarwa a cikin yakin.

Shugaban Asusun kananan yaran ya ci gaba da cewa; A kowance rana ta Allah kananan yara 130 ne suke mutuwa saboda yunwa da cutuka daban-daban da kuma yaki.

 Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa; A tsakanin mutane miliyan 20 da ake da su a kasar Yemen, kananan yara miliyan 11 ne suke da bukatuka da taimakon gaggawa.

Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yemen tun 2015 bisa cikakken goyon bayan Amurka da Birtaniya.