Iraki: Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutane 25
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27297-iraki_harin_ta'addanci_ya_ci_rayukan_mutane_25
Tashar talabijin din Iraki ta bada labarin cewa; A kalla mutane 25 ne suka mutu sanadiyyar harin kunar bakin waje biyu da aka kai a birnin Bagadaza
(last modified 2018-08-22T11:31:17+00:00 )
Jan 15, 2018 11:50 UTC
  • Iraki: Harin Ta'addanci Ya Ci Rayukan Mutane 25

Tashar talabijin din Iraki ta bada labarin cewa; A kalla mutane 25 ne suka mutu sanadiyyar harin kunar bakin waje biyu da aka kai a birnin Bagadaza

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Irakin ta ce an sami wasu mutane 63 wadanda suka jikkata sanadiyyar harin.

An kai harin ne dai a wata cibiya ta kasuwanci da take a birnin Bagadaza.

A watan da ya gabata ne dai gwamnatin kasar Iraki ta sanar da yin galaba akan kungiyar Da'esh.

Kungiyar ta Da'esh ta yi iko da wasu yankuna masu yawa na kasar Iraki da Syria gabanin a murkushe ta.