An Koma Teburin Tattaunawa Kan Rikicin Siriya A Vianna
Jan 25, 2018 06:48 UTC
Yau Alhamis ake komawa sabon zagayen tattaunawa kan rikicin kasar Siriya a birnin Vianna a shiga tsakanin MDD.
Wannan zama na kwanaki biyu na zuwa ne wata guda bayan wanda aka gudanar a birnin Genava, a ci gaba da neman mafita kan rikicin siyasa na kasar ta Siriya tsakanin wakilan 'yan adawa da na gwamnati.
An dai watse a taron da ya gabata wanda shi ne karo na takwas ba tare da cimma matsaya ba saboda kin amuncewar bangarorin na ganawa ta kud da kud.
Wakilin musamen na MDD kan rikicin kasar ta Siriya, Staffan de Mistura, ya bayyana zaman da ''mai matukar muhimmanci"
Tags