Qatar Ba Za Taba Kasancewa Karkashin Mallakar Saudiyya Ba_Al-Thani
Ministan harkokin wajen Qatar, Sheikh Mohamed ben Abderrahmane Al-Thani, ya fada cewa kasarsa ba zata taba kasancewa karkashin mallakar Saudiyya ba.
A wata hira da shafin yada labarai na Faransa '' Opinion internationale'', Al-Thani ya ce sun yi ammana cewa Saudiyya tana son Qatar ta kasance karkashin ikonta, to hakan ba zata taba samuwa ba.
Al-Tsani ya kara da cewa Qatar kasa ce mai tarihi dake daukar matakai bisa cin gashin kanta, wanda ba za'a taba tattaunawa a kai ba, don haka a cewarsa irin salon da Saudiyya take amfani da shi na neman karyamu ba zai yi wu ba, don kuwa Qatar da al'ummarta suna shirye don kare martabar kasar.
A ranar 5 ga watan Yuni na shekara data gabata ne kasashen da suka hada da Saudiyyar da Hadaddiyar daular Larabawa da Bahrein da kuma Masar suka katse huldar diflomatsiyyarsu kasar ta Qatar, bisa zarginta da taimakawa kungiyoyi masu tsatsaran ra'ayi musamen kungiyar 'yan uwa musulmi a Masar da kuma neman dasawa da kasar Iran, batun da Qatar ke ci gaba da musuntawa.
Kasashen sun kuma rufe iyakokinsu na sama dana ruwa da kasa tsakaninsu da Qatar din.
Qatar dai ta ce a shirye take tun farko don samun mafita ta hanyar diflomatsiya amma da sharadin mutunta 'yancin da take da shi da kuma dokoki na kasa da kasa.