Turkiyya : Zamu Ci Gaba Da Yakar Kurdawa _ Erdogan
Shugaba Recep Tayyip Erdogan, na Turkiyya ya ce kasarsa za ta ci gaba da farmakin da take kaiwa kan mayakan Kurdawa na (YPG) dak take dangantawa da 'yan ta'ada a yankin Afrin.
Mista Erdogan dai ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar ba zata da ya kai a bataliyar sojojin da aka jibge a yankin Hatay a iyaka da Siriya.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da Kurdawan suka nemi agajin gwmatin Bashar Al- Assad na Siriyar.
Farmakin da Turkiyyar ke ci gaba da kaiwa kan Kurdawan ya dada kara tabarbarewar dangantaka tsakanin Amurka da Turkiyya.
Amurka dai ta bukaci Turkiyya data samar da wasu tuddan mun tsira a iyaka da Siriya da kuma neman ta tsagaita hare-hare kan Kurdawan.
Farmakin da Turkiyya ke kaiwa dai na zuwa ne a daidai lokacin da sake komawa kan teburin tattaunawa kan rikicin kasar Siriya a birnin Vianna karkashin jagorancin MDD, wanda ake ganin halin da ake ciki zai yi tasiri a zaman.