Kurdawan Siriya Sun Bukaci Taimakon Gwamnatin Kasar Kan Turkiya
Turkawan kasar Siriya masu samun goyon bayan gwamnatin Amurka sun bukaci gwamnatin kasar da ta kawo masu dauki kan fatattakar su da sojojin kasar Turkiya suke yi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kiran na a matsayin wani ja-da-baya ne ga Kurdawan na Siriya wadanda kafin haka suke ganin yankin su ya fice daga kasar Siriya.
A wata sanarwa wacce gwamnatin yankin Afrin ta kurdawan kasar siriya ta fitar a jiya Alhamis , gwamnatin ta yi kira ga gwamnatin Syriya ta taimaka ta baza sojojinta kan iyakarta da kasar Turkiya ta kuma hana jiragen saman yakin Turkiya kai hare hare kan yankin na Afrin.
A dai-dai lokacin da kungiyar Daesh take mamaye da wasu yankunan kasar ta Siriya ne Kurdawan tare da taimakon Amurka suka kwace yankin nasu daga hannun Daesh suka shelanta cewa sun sami 'yanci kenan daga gwamnatin kasar Syria.
Labaran sun nuna cewa gwamnatin Amurka ta horar da mayakan kurdawan kasar ta Siriya kimanin dubu 30 don ta yi amfani da su wajen kifar da gwamnatin kasar Siriya, kuma tana da wani shiri na maida yankin wani tudun na tsira ga yan ta'adda amma har yanzun hakan bai tabbata ba.