Syria: Yaki Da Ta'addanci Fada Ne Da Sahayoniya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i27823-syria_yaki_da_ta'addanci_fada_ne_da_sahayoniya
Mai bada shawara ga shugaban kasar Syria Buthain Sha'aban ce ta bayyana haka a yayin taron da aka bude akan birnin Kudus, a birnin Damascuss.
(last modified 2018-08-22T07:01:22+00:00 )
Feb 01, 2018 03:26 UTC
  • Syria: Yaki Da Ta'addanci Fada Ne Da Sahayoniya

Mai bada shawara ga shugaban kasar Syria Buthain Sha'aban ce ta bayyana haka a yayin taron da aka bude akan birnin Kudus, a birnin Damascuss.

Sha'aban ta ci gaba da cewa; A daidai lokacin da kawancen gwagwarmaya a yankin gabas ta tsakiya yake samun galaba akan 'yan ta'adda, wasu kasashen da suke taimakawa 'yan ta'adda, sun fara aikewa da sojojinsu zuwa cikin kasar ta Syria.

Sha'aban ta kara da cewa; Sojojin Turkiya da Amurka sun shiga cikin kasar Syira ne saboda maye gurbin 'yan ta'addar da aka murkushe.

Shekaru bakwai kenan da Syria take fama da hare-haren ta'addanci da na kasashen Amurka da Turkiya.