Kashe Wutar Fitana Ta Baya-Bayan Nan A Kasar Lebanon
(last modified Tue, 06 Feb 2018 06:31:29 GMT )
Feb 06, 2018 06:31 UTC
  • Kashe Wutar Fitana Ta Baya-Bayan Nan A Kasar Lebanon

A ranar 29 ga watan Janairun da ya gabata ne wata fitana ta kunno kai a harkokin siyasar Kasar Lebanon wacce ta kai ga cacar baki tsakanin magoya bayan shugaban kasar Michel Aoun da kuma na Kakakin majalisar dokokin kasar Nabi Berri.

Da farko dai, an yada wani faifan bidiyo ne, inda a cikinsa Ministan harkokin wajen kasar, kuma surukin shugaban kasa Gebran Bassi, yake aibata kakakin majalisar dokokin kasar Nabi Berri kan batun nuna rashin amincewarsa, da yadda shugaban kasar ya karawa wasu sojojin kasar matsayi, mafi yawansu Kiristoci a cikin watan Disamban da ya gabata, ba tare da tuntubar ministan kudi na kasar, kuma dan shia, wato Ali Hassan Khalil, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada ba. 

Berri yana ganin hakan ya sabawa adalcin da ya kamata shugaban ya kiyaye tsakanin Musulmi da kirista a kasar. A cikin hotunan Bidiyon Gebran Bassil ya kira Nabi Berri da sunan "Dan Daba". Daga nan ne magoya bayan Berri suka fusata suka kuma yi ta zanga zangar neman Afwa daga Ministan harkokin wajen kasar dangane da wannan Furucin. 

Wani abu mai muhimmanci dangane da wannan rikicin shi ne, cewa yana faruwa tsakanin jam'iyyun da suke kawance a tsakaninsu da kuma kungiyar Hizbullah, sannan a dai dai lokacin da ake shirye shiryen gudanar da zabe majalisar dokoki a kasar a cikin watan Mayu mai zuwa.

Banda haka rikicin yana iya shafar gwamnatin hadakar kasar, wadda firaminista Sa'adul Hariri yake bukatar tallafin dukkan jam'iyyun siysar kasar don wanzuwarta. Bayan haka rikicin yana faruwa ne a dai dai lokacin da ake juyayin kisan tsohon firaministan kasar mahaifin Firaminista mai ci, wato Rafikul Hariri.

Kafin haka dai rikici tsakanin Shugaban kasar da kuma  Kakakin majalisar dokokin kasar ta Labanon ya dade, don yana da asali tun lokacin yakin basasar kasar.

Banda haka wakilan kungiyar Amal ta yan shia karkashin jagorancin Nabi Berri sun ki zaben Michel Aun a matsayin shugaban kasa a zaben sa da aka yi a cikin watan Oktoban shekara ta 2016 da ta gabata.

Dangane da kawo karshen wannan fitinar,  Jaridar "Al-Akbar" ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Sayyid Hassan Nasarallah babban sakataren kungiyar Hizbullah ne ya shiga tsakanin kawayensa biyu.

Sannan jaridar :"Annahar"  ita ma ta kasar Labanan ta ce "Abbas Ibrahim shugaban hukumar tsaro ta cikin gida, ya wakilci kungiyar Hizbullah don kashe wutar Fitinar. Annahar ta ce,  firaministan kasar Sa'adul Hariri tare da sauran bangarorin ne suka shiga tsakanin don kawo karshen wannin fitinar. 

Inda bayan wannan kokarin ne shugaban kasar ta Lebanon Michel Aun, a ranar Talatan da ta gabata ya bada hakuri wa kakakin majalisar dokokin kasar, kan abinda surukinsa kuma Ministan harkokin waje Gebran Bassil ya furta, sannan  ya bukaci dukkan bangarorin su yafewa juna kan wannan lamarin.  

Wani abu mai muhimmanci dangane da wannan fitinar, shi ne cewa firaministan kasar Sa'adul Hariri ya bayyana cewa babu wata hanyar da ta rage wa kasar Labanan in banda amincewa da matsayi mai girma wanda kungiyar Hizbullah take da shi, da kuma cewa tattaunawa da fahintar juna tare da ita, don  kai kasar Lebanon ga nasara. Furucin firaministan dai, ya nuna cewa mummunan shirin kasar Saudia a kasar Lebanon, ya kasa kaiwa ga nasara. Musamman a kokarinta na ganin an maida kungiyar Hizbullah saniyar ware a harkokin siyasar kasar ta Lebanon.