Isra'ila: An nemi gurfanar da Netanyahu kan rashawa
(last modified Wed, 14 Feb 2018 11:58:39 GMT )
Feb 14, 2018 11:58 UTC
  • Isra'ila: An nemi gurfanar da Netanyahu kan rashawa

Dariruwan mazauna birnin Tel-Aviv na HK Isra'ila sun taru a gaban gidan Firaminista Benjamin Netanyahu, inda suka nemi a gurfanar da shi a gaban shari'a saboda laifuka na cin hanci da rashawa da kuma zamba cikin aminci.

Wannan bore na zuwa ne bayan 'yan shekaru ana binciken zargin da ake wa Firaiministan na amsar rashawa daga wasu abokansa yayin da shi kuma ke basu ayyuka na musanman, akwai kuma zargin da jami'an tsaron suka yi masa kan yin katsalandan a harkokin wasu kafaffen yada labarai da ya fifita fiye da saura.

Tuni dai Firaminista Netanyahu ya musanta wadannan zarge-zargen da ya ce yunkuri ne na ganin an tilasta masa sauka daga karagar mulki, a cewarsa wannan ba shi bane karon farko da ake kira shi a tuhume shi kan laifukan da bai aikata ba.

Yanzu dai ana sa ran mika koken 'yan kasar gaban lauyan gwamnati, a yayin da jam'iyyun adawa a daya bangaren suka bukaci Netanyahu da ya yi murabus daga mukaminsa.