Mahmoud Abbas Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Amince Da Kasar Palasdinu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i28401-mahmoud_abbas_ya_bukaci_kasashen_duniya_su_amince_da_kasar_palasdinu
Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas, ya yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya kira taron kasa da kasa wanda zai kai ga amincewa da kasar Palasdinu bisa yarjejeniyar kan iyaka ta shekarar 1967 da aka shata.
(last modified 2018-08-22T11:31:27+00:00 )
Feb 21, 2018 05:54 UTC
  •  Mahmoud Abbas Ya Bukaci Kasashen Duniya Su Amince Da Kasar Palasdinu

Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas, ya yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya kira taron kasa da kasa wanda zai kai ga amincewa da kasar Palasdinu bisa yarjejeniyar kan iyaka ta shekarar 1967 da aka shata.

Shugaba Abbas ya ce, al'ummar Palasdinu na kira ga kwamitin sulhun MDD da ya gaggauta kiran taron kasa da kasa a tsakiyar wannan shekara, kamar yadda dokokin kasa da kasa da kudurorin MDD suka tanada.

Abbas ya yi watsi da duk wani wunkuri na Amurka kawai a matsayin mai shiga tsakani a shirin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

A hannun guda kuma, Shugaba Abbas ya bukaci sakamakon taron ya amince da kasar Palasdinu a matsayin cikakkiyar mambar MDD.

Bugu da kari, shugaban Palasdinun ya bukaci Birnin Qudus ya zamo kofa bude ga dukkan addinai guda uku, tare da neman kuma birnin na Qudus da ya zama babban birnin kasar ta Palasdinu a nan gaba.