Siriya : Ana Ci Gaba Da Kiran Tsagaita Wuta A Gabashin Ghouta
Kungiyar Tarayya Turai ta yi kira da babbar murya akan a tsagaita buda wuta a yankin gabashin Ghouta na Siriya, a daidai lokacin da kwamitin tsaro ke shirin kada kuri'a kan samar da shirin tsagaita wuta a wannan yankin.
Kafin hakan dama shugaban kasar Faransa da takwararsa ta Jamus, Angela Merkel, sun aike da wasika ga shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, akan ya amunce da kudirin na tsagaita wuta.
Babbar jami'ar kula da harkokin waje ta EU, Federica Mogherini, dake halartar taron kungiyar G5 a Brassuls, ta ce bata san yadda za ta kwatantan ba'ain da shiga yankin na Ghouta ba, don haka ya kamata a dakatar hakan ba tare da wata-wata ba.
Da yammacin nan ne kwamitin tsaro na MDD zai kada kuri'a kan kudirin tsagaita na tsawan kwanaki 30 a yankin na Ghouta domin bada damar shigar da kayan agaji.
Wasu alkalumma da MDD ta fitar sun nuna cewa tun daga ranar Lahadi kawo yanzu, a kalla fararen hula 436 ciki har da yara 99 ne suka rasa rayukansu hare-hare mafi tsanani da dakarun gwamnatin Siriya ke ci gaba da kaiwa kan 'yan tada kayar baya a yankin.