Kungiyar EU Ta Kakaba Wa Ministocin Gwamnatin Siriya Takunkumin Tattalin Arziki
(last modified Tue, 27 Feb 2018 08:09:27 GMT )
Feb 27, 2018 08:09 UTC
  • Kungiyar EU Ta Kakaba Wa Ministocin Gwamnatin Siriya Takunkumin Tattalin Arziki

Majalisar dokokin kungiyar tarayyar Rurai ta dorawa minitocin gwamnatin kasar Siria guda takunkuman tattalinn arziki.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayyana cewa a zaman da majalisar ta tarayyar turai ta gudanar a jiya Talata ta amince da dorawa ministan masana'antu da kuma sadarwa na halittaccen gwamnatin kasar Siria tukunkumai.

Labarin ya kara da cewa a cikin watan Jenerun shekarar da ta gabata ce shugaba Bashar al-asad ya nada Ali Yusuf a matsayin ministan tattalin arzikin kasar a yayinda ya nada Emad Abdullahi Sare a matsayin ministan harkokin sadarwa na kasar.

Banda wadannan ministoci, majalisar ta dorawa wasu manya manyan mutanen kasar da Siria da dama takunkumai da sunan suna goyon bayan ayyukan ta'addanci. 

Tun shekara ta 2011 ne kasashen yamma da kuma kawayensu na yankin suke tunzara mutanen kasar Siria don kifar da gwamnatin Bashar Al-asad amma bayan sun kasa samun nasara suka koma kan dorawa gwamnatin takunkuman tattalin arziki.