Syria: "Yan Ta'adda Suna Shirin Amfani Da Makamai Masu Guba
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i28705-syria_yan_ta'adda_suna_shirin_amfani_da_makamai_masu_guba
A jiya alhamis ne ma'aikatar tsaron kasar Syria ta sanar da cewa; 'yan ta'addar da ke Ghuta suna shirin amfani da makamai masu gubar domin su dora wa gwamnati alhaki.
(last modified 2018-08-22T07:01:30+00:00 )
Mar 02, 2018 03:17 UTC
  • Syria:

A jiya alhamis ne ma'aikatar tsaron kasar Syria ta sanar da cewa; 'yan ta'addar da ke Ghuta suna shirin amfani da makamai masu gubar domin su dora wa gwamnati alhaki.

Ma'aikatar tsaron ta ci gaba da cewa; Kasashen Amurka da Birtaniya da  wasu kasashen yammacin turai sun ba da umarni ga 'yan ta'addar kungiyar Nusrah da ke Ghuda akan su yi amfani da makamai masu guda idan suna fada da sojojin gwamnati, domin a fito da wani sabon salon shiri.

Yankin Ghuda wanda yake kusa da birnin Damascus yana daga cikin yankunan da 'yan ta'adda suke da sansani, wanda su ke amfani da shi wajen harba makamai masu linzami akan babban birnin kasar.

A wani gefen ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar da sanarwa da a ciki ta ce; Manufar Amurka da kawayenta shi ne jinginawa gwamnatin Syria hari da makamai masu guba da 'yan ta'adda za su kai.