Syria: 'Yan Ta'adda Suna Hana Fararen Hula Ficewa Daga Ghuta
Cibiyar Suhlu ta Rasha a kasar Syria ta sanar da cewa; 'Yan ta'addar sun rika kai hari da manyan bindigogi akan wuraren da aka ware domin ficewar fararen hula
Janar VIlademir Zolotokhin wanda shi ne kakakin cibiyar sulhult masu fada da juna a kasar Syria, ya fada a yau lahadi cewa; "Yan ta'adda sun yi amfani da manyan bindigogi wajen kai hari akan yankin al-Raihan, sai dai babu wata asara da harin ya haifar.
Janar vieademir ya kuma ce; Har yanzu 'yan ta'addar suna ci gaba da yin tsokana da keta yarjejeniyar tsagaita wuta. Har ila yau jami'in sojan na Rasha ya zargi 'yan ta'addar da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da kudurin tsagaita wuta na kwanaki 30 wacce ta fara aiki tun a ranar litinin ta makon da ya wuce.
Sai dai yarjejeniyar ta bai wa sojojin Syria damar ci gaba da yaki da 'yan ta'adda.