Afganistan : Harin Ta'addanci Ya Yi Ajalin Mutum 9 A Kabul
Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane a kalla 9 ne suka rasa rayukansu a wani harin ta'addanci da aka kai a kusa da wani masallaci dake Kabul babban birnin kasar.
Wata sanarwa da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar a yau Juma'a, ta ce an kai harin ne a kusa da wani shingen bincike, kuma harin ya rusa da jami'an 'yan sanda biyu da kuma wasu fararen hula bakwai, a yayin da mutane 22 suka raunana.
Bayanai sun ce an kai harin ne a wajen wani taron juyayin zagayowar shekaru 23 da shahadar wani jagoran 'yan shi'a mai suna Abdul Ali Mazari da 'yan taliban suka kashe, wanda kuma wasu manyan jami'an kasar ta Afganistan ke halarta.
Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta fitar da sanarwar cewa ita ke da alhakin kai harin na yau Juma'a.
Wasu alkalumma da MDD ta fitar sun nuna cewa sama da mutane 10,000 ne suka suka jikkata ko aka kashe a cikin 2017 data gabata a rikicin da wannan kasa ta Afganistan ke fama da shi.